Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Auna ya fadi cewa kundin tsarin mulkin kasar shi ne kwai mafita ga matsalolin da kasar ke fuskanta amma ba za’a amince da yin amafani da makami kan masu zanga-zanga ba, domin gwamnati ta bada yanci fadin albarkacin baki
Wannan yana zuwa ne bayan da wasu al’ummar kasar Labanon suna gudanar da zanga- zangar lumana ta nuna rashin amincewa da matakin da Tariq Bitar alkalin da ke bincike kan fashewar gabar tekun Berut yake dauka da ya afku a watan Agustan shekara ta 2020 da ta gabata, inda wasu masu dauke da makamai daga saman bene suka bude wuta kan masu zanga zangar tare da kashe mutane 6 da kuma jikkata fiye da 60,
Kungiyar hizbullah da Amal da ke kasar Labanon sun bukaci magoya bayansu da su kwantar da hankalim kada su dauki doka a hannu kan harin da magoya bayan Jam’iyar AlQuwwat Alibananiya wato Labanes Forcess suka kai kan masu zanga zangar.
342/